Najeriya : Za'a kawo karshen Karancin mai A Watan Afrilu Inji Kachikwu
Mar 30, 2016 05:22 UTC
Ministan ma'aikatar mai ta Najeriya Dr Emmaneul Ibe Kachikwu, ya bayyana cewa a cikin watan Afrilu za'a kawo karshen karancin man da ake fama da shi a kasar.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin kula da harkokin man fetur na Majalisar dattawan kasar a ranar Talata 29 ga wata, domin ya amsa tambayoyi a kan matsalar karancin man fetur din da ake fuskanta a wasu sassan kasar.
Wakilin mu a Abuja Muhammad Sani Abubakar ya hada muna wannan rahoto
Tags