Najeriya : Majalisun Dokoki Sun Gindaya Wa Gwamnatin Buhari Bukatu 12
Majalisun dokokin tarayya Najeriya da suka hada da ta Dattawa da ta Wakilai, sun gindaya wa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, da jerin bukatu 12, ko kuma su dau mataki kan gwamnatin.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki ne ya karanta matsayar da suka cimma bayan wani zama na musamman da suka yi yau, domin duba halin da kasar take ciki.
Majalisun sun yi barazanar amfani da karfin da kundin tsarin mulki ya basu, wajen daukar mataki kan shugaban kasar, muddin yaki amincewa da bukatunsu.
Bukatun sun hada da, kawo karshen kashe-kashe a fadin kasar, da daina tsangwama da muzguna wa wadansu 'yan majalisa, kana kuma gwamnatin ta rika bin doka da oda.
Sauran bukatun kuma sun hada da Shugaban kasar ya dauki mataki kan wadansu wadanda ya nada mukamai, sannan ya yi yaki da cin hanci da rashawa tsakaninsa da Allah, ya kuma daina tsoma baki kan al'amurran da suka shafi majalisar.
A daya sharen kuma majalisoshin biyu sun nuna goyon baya ga shugabancin Bukola Saraki da kuma Yakubu Dogara, sannan sun ce ba sa goyon shugabancin Sufeto Janar na'yan sandan kasar Ibrahim Idris.
Wannan dai na zuwa ne bayan da a ranar Litinin din nan 'yan sandan kasar suka gayyaci Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki domin amsa tambayoyi kan zargin daukar nauyin 'yan fashi da makami a mahaifarsa ta jihar Kwara, koda yake daga baya sun janye gayyatar, suna masu bukatar ya bada amsa a rubuce.