Najeriya : Yawan Masu Fama Da Cutar Kwalera Ya Haura Dubu
Hukumomin kiwan lafiya a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya sun ce, adadin mutanen da cutar amai da gudawa ko kwalera ta kama a jihar, ya haura dubu guda.
Kawo yanzu dai mutane 18 ne aka rawaito cutar ta yi ajalinsu a jihar ta Adamawa.
Tuni dai hukumar lafiya ta duniya WHO, ta fara gudanar da wani gangamin dakile yaduwar cutar na kofa kofa a birnin Mubi, domin ganowa da kuma fadakar da jama'a kan hanyoyin hana yaduwar cutar.
Jami'in dake lura da shirin Kabiru Sadiq, ya ce matakan gaggauwa da ake dauka sun bada damar gano sabbin masu kamuwa da cutar, wanda hakan ya taimaka gayan wajen tasirin da cutar take da shi na hallaka al'umma, inda yawan masu rasuwa sakamakon kamuwa kamuwa da cutar ta amai da gudawa ko kwalera ya ragu daga kaso 17 bisa dari zuwa kaso 1.7 bisa dari.
Masana kiwon lafiya dai sun ce ana daukar kwayar cutar ne ta rashin safta, musamman cin abinci da hannu ba tare da an wanke sosai ba.