Buhari: Nijeriya Za Ta Karfafa Alakar Tattalin Arziki Da Kasar Tanzaniya
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar Nijeriya a shirye ta ke ta kara karfafa alakarta ta tattalin arziki da kasar Tanzaniya don amfanin dukkanin kasashe biyun.
Shugaba Buharin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karba takardar kama aikin jakadar kasar Tanzaniya a Nijeriya, Muhidin Moweto, a fadar shugaban kasa ta Aso Rock da ke Abuja, inda ya ce dukkanin kasashen biyu suna da abubuwan da za su iya sanya su su zamanto masu fadi a ji a fagen tattalin arziki a yankunan da suke.
Shi ma a nasa bangaren, sabon jakadan na Tanzaniya ya bayyana farin ciki da kuma jinjinawar kasarsa dangane da irin kokarin da Nijeriya da kuma kamfanonin kasar suke yi wajen karfafa kasar Tanziyya da kuma tattalin arzikinta, yana mai jaddada aniyarsa ta yin duk wani abin da zai iya wajen ganin alakar da ke tsakanin kasashen biyu ta kara karfafuwa.
Har ila yau jami'in jakadancin ya isar da sakon jinjinawar shugaban Zanzibar, wani yanki na kasar Tanzaniya da ke da kwarya kwaryar cin gashin kai, saboda tura malamai 41 da gwamnatin Nijeriya ta yi zuwa can don taimaka ma'aikatar ilimin kasar.