Najeriya : 'Yan Bindiga Sun Sace Matafiya Sama Da 30 A Kaduna
Rahotannin daga Najeriya, na cewa an kashe matafiya biyu, kana kuma an yi garkuwa da wasu sama da 30, a kan hanyar jihar Kaduna, dake yankin arewa maso yammacin kasar.
Wasu majiyoyi sun ruwaito cewa, daga cikin wadanda aka sace akwai wata mace da jaririyarta, kuma tuni aka bukaci iyalanta dasu biya kudin fansa Naira Miliyan biyar.
Matafiyan na tafiya ne a kan titin nan mai hadari na Birnin-Gwari dake Kaduna, a lokacin da 'yan bindigar suka tsaida su a kwanar-tsauni, dake tsakanin kauyukan Udawa da Labi dake yankin.
Wani direban motar haya da al'amarin ya auku kan idonsa mai suna Mohammed Kebi, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren Xinhua cewa a kalla motoci 5 masu satar mutanen suka tsare da misalin karfe 11 na safiyar jiya Jumma'a.
Matsalar garkuwa da mutane a wannan kasa ta Najeriya ta zama gagara badau musamman a wannan yankin, inda ko a watan Mayu da ya gabata mutane a kalla 100 akayi garkuwa dasu a cikin kwanaki biyu kacal.