An ware $ million 7 don taimakawa 'yan gudun hijrar Sudan Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i316-an_ware_million_7_don_taimakawa_'yan_gudun_hijrar_sudan_ta_kudu
Majalisar Dinkin Duniya Ta ware $ million 7 don taimakawa 'yan gudun hijrar Sudan Ta Kudu
(last modified 2018-08-22T06:57:46+00:00 )
Feb 05, 2016 05:17 UTC
  • An ware $ million 7 don taimakawa 'yan gudun hijrar Sudan Ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya Ta ware $ million 7 don taimakawa 'yan gudun hijrar Sudan Ta Kudu

Shafin Internet na Sudan Taribun ya habarta cewa, Asusun dake kula da rikice-rikiice na MDD ya ware $ million 7 domin taimakawa 'yan gudun hijrar Sudan ta kudu dake sansanin 'yan gudun hijra na kasar Sudan.

Rahoton ya ce Sama da Mutanan sudan ta kudu dubu 198 ne da raikicin yakin cikin gida ya raba da mahalinsu ke gudun hijra a kasar ta Sudan kuma mafi yawanzu na zaune a yankin Nil Safid da kuma Khartum babban birnin kasar.

Muhamad Adar wakilin babban kwamishinan 'yan gudun hijra na MDD ya bayyana cewa a wannan maku mai kamawa ne za mu karbi kudin domin biyan bukatun 'yan gudun hijrar a bangaren kiyon lafiya, abinci da kuma bangaren ilimi.

Gwamnatin jihar Nil Aby ta ware sansanin 'yan gudun hijra 7 ga 'yan gudun hijrar na Sudan ta kudu, inda yanzu haka sansanonin suka cika makil, lamarin da ya sanya Gwamnatin ta bukaci taimako daga MDD.