Afirka Ta Tsakiya : Faustin Touadera Yayi Rantsuwar Kama Aiki
Sabon shugaban Afrika ta Tsakiya Faustin Touadera yayi rantsuwar kama aiki a wani katsatacen biki da aka gudanar yau Laraba a Bangui babban birnin kasar.
Sabon shugaban da yayi nasara a zaben da aka gudanar a cikin watan jiya, yayi alkwarin mutunta kundin tsarin mulkin kasar ba tare da nuna banbanci akida ko addini ba.
Touadera mai shekaru 58 zai shugabanci wannan kasa ce da ta share tsawon shekaru tana fama da tashe-tashen hankula da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma rabuwar kawuna a tsakanin kabilu da kuma mabiya addinai.
An dai gudanar da bikin ne tare da halartar wakilai daga MDD da baki daga kasashen ketare da dama ciki harda Faransa wace a ta bakin Ministan tsaron ta Jean-Yves Le Drian ta sanar da cewa, zata janye sojojin ta a wannan kasa cikin wannan shekara domin sunyi iyakacin kokarinsu wajen tababtar da zaman lafiya a wannan kasa, duk kuwa dai da cewa akwai sauran 'yan matsaloli a gaba.