An Gargadi HKI Kan Shiga Rikicin Yankin Darfur Na Sudan
Jam'iya mai milki ta kasar Sudan ta gargadi yahudawan sahayuwa da samar rashin tsaron a yankin Darfur.
Hukumar gidan talabijin da radio na kasar Iran ya nakalto Ali Haj babban saktaren jam'iya mai milki ta kasar Sudan na gargadin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da yin katsa landan a rikicin Jabalu marra na yankin Darfur, inda yake cewa katsa landan din da yahudawan sahayuna ke yi a yankin ta hanyar wasu kungiyoyin kasa da kasa na kokarin kunna wuta a yankin domin cimma wasu manufofinsu.
Ali Haj ya bukaci gwamnati da ta gaggauta zartar da shirinta na wanzar da sulhu a yankin domin kadda yankin na Darfur ya sake fadawa cikin rikici.
Yankin Darfur dai na daga cikin yankunan masu karamin karfi a kasar ta Sudan da ya kwashe shekara da shekaru cikin yaki, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwa da kuma hijra na duban mutanan yankin.
Mazauna yankin Darfur dai na zarkin gwamnati da mayar da su saniyar ware a bangaren siyasa da tattalin arziki, kuma tun daga shekarar 2003 ne yankin ya fada cikin rikici, a shekarar 2016, gwamnati ta sanar da shirin tsagaita wuta a yankin.