Kenya: Harin Ta'addanci Ya Ci Rayukan Mutane 7
Jun 18, 2018 12:12 UTC
Kakakin 'yan sandan kasar Kenya Charles Oyino ne ya sanar da cewa an dasa bom din ne a bakin hanya a gabacin kasar wanda kuma ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai
Majiyar ta ce; An nufi jami'an 'yan sanda da suke sintiri ne da kai hari.
A farkon wannan watan na Yuni an kashe jami'an 'yan sandan kasar ta Kenya biyar ta hanayr harin ta'addanci.
Yankunan arewaci da kuma gabacin kasar Kenya sun zama inda kungiyar al-Shabab take kai wa hare-haren ta'addanci.
Kasar Kenya tana cikin kasashen da suka aike da sojojinsu zuwa kasar Somaliya domin fada da kungiyar al-shabab.
Kungiyar ta al-shabab tana a matsayin barazanar tsaro ga kasar Somaliya da kuma kasashen makwabta da su ka hada da Kenya.
Tags