Najeriya: Yawan Mamata A Harin Borno ya Karu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31852-najeriya_yawan_mamata_a_harin_borno_ya_karu
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato majiyar tsaron Najeriya na cewa; Adadin wadanda su ka kwanta damar sanadiyyar harin da aka a garin Damboa ya kai 43.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jun 19, 2018 08:31 UTC
  • Najeriya: Yawan Mamata A Harin Borno ya Karu

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato majiyar tsaron Najeriya na cewa; Adadin wadanda su ka kwanta damar sanadiyyar harin da aka a garin Damboa ya kai 43.

A sanarwar farko an ce mutane 31 ne su ka kwanta dama yayin da wasu da dama su ka jikkata.

Harin da aka kai na kunar bakin wake ne wanda ake gangantawa kungiyar Boko Haram.

Tun a 2009 ne dai kungiyar ta Boko Haram take kai hare-haren ta'addanci a Najeriya da kasashen makwabta da su ka hada Nijar, Kamaru, da Chadi.

Kawo ya zuwa yanzu kungiyar ta kashe mutanen da su ka kai 20,000, sai kuma wasu miliyan biyu da 600,000 da su ka zama 'yan gudun hijira.