Majalisar Dinkin Duniya Ta Kara Wa'adin Zaman Dakarunta A Kasar DR Congo
Majalisar Dinkin Duniya ta kara wa'adin zaman dakarunta da suke aikin wanzar da zaman lafiya da sulhu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na tsawon shekara guda.
A zaman da ta gudanar a jiya Laraba: Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakin kara wa'adin ci gaba da zaman dakarunta da suke aikin wanzar da zaman lafiya da sulhu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na tsawon shekara guda tare da jaddada yin kira ga mahukuntan kasar da su gudanar da zabuka cikin gaskiya da 'yanci a duk fadin kasar.
Yau tsawon shekaru 16 ke nan da jibge dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo lamarin da wasu mahukuntan kasar ke ganin lokaci yayi da za a sakarwa jami'an tsaron Dimokaradiyyar Congo ragamar wanzar da zaman lafiya da sulhu a kasarsu musamman ganin a halin yanzu an shawo kan manyan matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta.