Najeriya : Buhari Ya Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudin 2018
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31904-najeriya_buhari_ya_rattaba_hannu_kan_kasafin_kudin_2018
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin kasar na shekarar 2018 a jiya Laraba, 'yan makwanni kadan bayan da majalisar dattawan kasar ta amince da shi.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jun 21, 2018 01:24 UTC
  • Najeriya : Buhari Ya Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudin 2018

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin kasar na shekarar 2018 a jiya Laraba, 'yan makwanni kadan bayan da majalisar dattawan kasar ta amince da shi.

Rahotannin sun nuna shugaban ya sanya hannun ne a ofishinsa da ke fadarsa ta Villa a Abuja babban birnin kasar.

Sai dai shugaban ya nuna damuwa matuka kan wasu sauya-sauye da ya ce majalisar kasar ta aiwatar a kasafin na 2018.

Shugaba Buhari ya ce bai ji dadin yadda majalisar ta rage kasafin da kusan Naira biliyan 350 na wasu ayyuka 7,700 yayinda suka gabatar da wasu ayyuka 6,403 na kashin kansu da zai lakume Naira biliyan 578.