Najeriya: Ana Ci Gaba Da Zanga-zangar Neman Sakin Sheikh Elzakzaky
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31908-najeriya_ana_ci_gaba_da_zanga_zangar_neman_sakin_sheikh_elzakzaky
A jiya Laraba ne Mambobin Harkar Musulunci Su ka yi Zanga-zanga a birnin Kaduna suna masu kiran da a saki jagoransu Sheikh Ibrahim Yakubu El-zakzaky
(last modified 2018-08-22T07:02:00+00:00 )
Jun 21, 2018 07:34 UTC
  • Najeriya: Ana Ci Gaba Da Zanga-zangar Neman Sakin Sheikh Elzakzaky

A jiya Laraba ne Mambobin Harkar Musulunci Su ka yi Zanga-zanga a birnin Kaduna suna masu kiran da a saki jagoransu Sheikh Ibrahim Yakubu El-zakzaky

Kamfanin dillancin labarun Fars na iran ya amabato kafafen watsa labarun Najeriya na nuni da cewa jami'an tsaro sun yi amfani da karfi wajen dakile Zanga-zangar inda suka jikkata wasu da dama.

A cikin watannin bayan nan Jahar kaduna ta zama inda mambobin harkar musuluncin suke yin Zanga-zangar neman sakin Sheikh El-Zakzaky baya ga babban birnin tarayya Abuja.

Tun a cikin watan Disamba na 2015 ne aka kama Sheikh El-Zakzaky tare da mai dakinsa Zenat  bayan mummunan harin da sojojin kasar su ka kai a gidansa.

 Bugu da kari harin ya yi sanadin mutuwar daruruwan almajiran shehun malamin da kuma 'ya'yansa.