Najeriya: An Dage Zaman Shari'ar Sheikh Zakzaky A Kaduna
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31924-najeriya_an_dage_zaman_shari'ar_sheikh_zakzaky_a_kaduna
An dage zaman sauraren shari'ar Sheikh Zakzaky da aka shirya gudanarwa a yau a Kaduna sakamakon rashin halartar alkali.
(last modified 2018-08-22T07:02:00+00:00 )
Jun 21, 2018 15:40 UTC
  • Najeriya: An Dage Zaman Shari'ar Sheikh Zakzaky A Kaduna

An dage zaman sauraren shari'ar Sheikh Zakzaky da aka shirya gudanarwa a yau a Kaduna sakamakon rashin halartar alkali.

Dubban magoya bayan Harkar musulunci ne suka taru a kaduna, inda suka gudanar da jerin gwanon yin kira da a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky, wanda hakan ya zo ne daidai da ranar sauraren shari'arsa a Kaduna, duk kuwa da cewa alkalin da ke shari'ar bai halarci zaman kotun ba.

Jami'an tsaro sun yi amfani da karfi domin hana magoya bayan Harkar musulunci gudanar da jerin gwanon

Shafin Sahara Reporters ya ce akalla magoya bayan harkar musulunci uku ne suka rasa rayukansu gami da dan sanda guda.

An sanar da sake dage shari'ar sheikh Zakzaky zuwa ranar 11 ga watan Yuli mai kamawa, kamar yadda lauyoyinsa suka tabbatar.