MDD: Ana Samun Cikas Wajen Ayyukan Agaji A Yankin Darfur Na Sudan
Majalisar dinkin duniya ta nuna damuwa kan matsalolin da ake samu wajen gudanar da ayyukan agaji a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya habarta cewa, tawagar majalisar dinkin duniya da ke gudanar da ayyukan agajia kasar Sudan ta sanar da cewa tana fuskantar matsaloli masu tarin yawa wajen gudanar ayyukanta a yankin Darfur, tare da bayyana cewa gwamnatin Sudan ce da kanta take kawo tarnaki a aikin nasu.
Bayanin ya ce a halin yanzu akwai matsalolin tsaro a yankin na Darfur, inda kungiyoyin 'yan bindiga masu adawa da gwamnati da kuma masu mara mata baya suke fada da juna, inda kuma sukan kai hare-hare kan dakarun majalisar dinkin duniya da suke ayyukan wanzar da zaman lafiya, kamar yadda kuma hakan ya kan shafi ayyukan agaji da ake gudanarwa a yankin.