Al'ummar Masar Na Ci Gaba Da Bayyana Adawarsu Da Siyasar Al-Sisi
Matsin tattalin arziki da al'ummar kasar Masar ke fuskanta ya sanya suna ci gaba da bayana rashin amincewarsu da siyasar shugabar kasar Al-Sisi a shafukan sada zumunta.
Kamfanin dillancin labaran Pars ya nakalto kafafen sadarwar kasar Masar na cewa kimanin 'yan kasar dake mu'amala da kafar sadarwar Twitwer ke bukatar Shugaba Al-Sisi ya yi murabus, saboda ya kasa magance matsalar siyasa da tattalin arzikin kasar.
Har ila yau 'yan kasar sun nuna fishinsu kan matakin baya-bayan nan da gwamnati ta dauka na kara farashiin man fetir, duk kuwa da alkawarin da shugaba Al-Sisi ya dauka na cewa ba zai kara ko sisi ba a yayin da yake yakin neman zabe a wa'adi na biyu.
Rahotani dake fitowa daga kasar ta Masar na nuni da cewa al'ummar kasar ba su ji dadi ba game da matakin da gwamnati ta dauka na kara farashin man fetir a kasar, inda suka ce wannan zai kara matsin lamba ga rayuwar al'ummar kasar, musaman ma masu karamin karfi.
Daga lokcin da Shugaba Abdulfatah Al-Sisi ya hau kan karagar milkin kasar Masar a shekarar 2014 zuwa yanzu talauci, rashin aiki yi, da kuma bashi kasashen waje ke kara karuwa ga kasar ga kuma yadda kudin kasar ke kara rage daraja.