Sudan Ta Soki Kotun Kasa Da Kasa Ta Manyan Laifuka
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta ce; Babu wani sakamako da ya fito daga kwamitin tsaro na MDD Akan rahoton kotun manyan laifuka ta kasa da ka dangane da yankin Darfur,
Kamfanin dillancin labarun Sputnic ya ambato ministan harkokin wajen kasar ta Sudan Qaribullah al-Khidhir yana cewa; Tare da cewa kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya ya saurari rahoton karo na 27, amma kawo ya zuwa yanzu babu wani kuduri ko kuma wata sanarwar da ta fito daga gare shi.
Al-Khidhr ya ci gaba da cewa; Yadda kotun kasa da kasa ta manyan laifuka ke gudanar da ayyukanta yana tattare da shakku sannan kuma yana nuni da shigar da siyasa a ciki domin yin tasiri a harkokin cikin gidan wasu kasashe.
Babbar mai shigar da kari ta kotun manyan laifukan Fatou Bensouda ta fadawa kwamitin tsaron majalisar Dinkin Duniya cewa wajibi ne a dauki dukkanin matakan da ya kamata domin kame shugaban kasar Sudan, Umar Hassan al-Bashir.
Tun a 2009 ne dai kotun ta manyan laifuka ta zargi shugaban kasar Sudan da aikara laifukan yaki da kisan kiyashi a yankin Darfur da ke yammmacin kasar