Zimbabwe : 2 Daga Cikin Mutane 49 Da Suka Raunana Sun Mutu
A Zimbabwe, an sanar da mutuwar mutum 2 daga cikin 49 da suka raunana a harin da aka kai a yayin gangamin yakin neman zabe na Shugaban kasar, Emmerson Mnangagwa.
Daya daga cikin mutanen biyu, jami'in rundinar tsaron fadar shugaban kasar ne.
Shugaba Mnangagwa, ma dai ya tsallake rijiya da baya a yayin harin, da aka kai a yayin gangaminsa na yakin neman zabe na farko, wanda ya danganta da yunkurin kashe shi.
Al'amarin dai ya auku a ranar Asabar data gabata, a birnin Bulawayo dake kudancin kasar inda 'yan adawa suka fi rinyaje.
Bayan aukuwar lamarin, shugaban kasar ya bayyana cewa harin ba zai kawo cikas ga shirin zaben kasar ba, za'a gudanar da zaben a ranar 30 ga wata Yuli mai zuwa kamar yadda aka tsara.