Shugabannin 'Yan Sanda Na Kasashen ECOWAS Na Taro Kan Yaki Da Ta'addanci
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32050-shugabannin_'yan_sanda_na_kasashen_ecowas_na_taro_kan_yaki_da_ta'addanci
Shugabannin 'yan sanda da kuma na tsaro na kasashen mambobin kungiyar raya arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS/CEDEAO, sun fara wani taron na yini uku a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast mai manufar karfafa hadin guiwa don yaki da ta'addanci.
(last modified 2018-08-22T07:02:01+00:00 )
Jun 26, 2018 01:24 UTC
  • Shugabannin 'Yan Sanda Na Kasashen ECOWAS Na Taro Kan Yaki Da Ta'addanci

Shugabannin 'yan sanda da kuma na tsaro na kasashen mambobin kungiyar raya arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS/CEDEAO, sun fara wani taron na yini uku a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast mai manufar karfafa hadin guiwa don yaki da ta'addanci.

Ministan cikin gida na Ivory Coast, Sidiki Diakita, ay bayyana a gun taron cewa, wannan haduwar babbar dama ce da za'a iya amfani da ita idan aka yi la'akari da yanayin da ake ciki yanzu ta fuskar tsaro a yankin.

Taron zai duba hanyoyin da kasashen mambobin kungiyar zasuyi hadin gwiwa ta fuskar aikin 'yan sanda da sha'anin shari'a ta yadda jama'ar yankin zasu samu 'yancin walwala.

Masana sha'anin tsaro a Afrika da dama na ganin cewa, yaki da ta'addanci shi ne a sahun gaba a cikin matakan dake bukatar hadin guiwa a tsakanin kasashen mambobin kungiyar ta yammacin Afrika, don dakile ayyukan ta'addanci.