Sharhi: Tattaunawar Sulhu Tsakanin Gwamnatin Sudan Ta Kudu Da 'Yan Tawaye
(last modified Tue, 26 Jun 2018 07:15:42 GMT )
Jun 26, 2018 07:15 UTC
  • Sharhi: Tattaunawar Sulhu Tsakanin Gwamnatin Sudan Ta Kudu Da 'Yan Tawaye

A daren jiya ne aka fara gudanar da tattaunawar sulhu zagaye na biyu tsakanin gwamnatin kasar Sudan ta kudu da kuma bangaren 'yan tawayen kasar a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan.

An shiga zagaye na biyu ne a wannan tattaunawa, bayan kasa cimma wata matsaya a zagaye na farko da aka gudanar a ranar Alhamis da ta gabata a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, karkashin jagorancin Firayi ministan kasar ta Habasha Abiy Ahmad.

Kungiyar bunkasa harkokin tattalin arzikin kasashen gabashin Afirka IGAD ce take sanya ido kan tattaunawar, inda a jiya shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu, da kuma madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar, tare da shugaban kasar Sudan Umar Hassan Alabshir, gami da shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, suka gudanar da zama a birnin Kahrtum.

Wannan tattauna za ta kwashe tsawon makonni biyu ana gudanar da ita, da nufin samo hanyoyin kawo karshen rikicin da kasar Sudan ta kudu take fama da shi tun daga karshen shekara ta 2013, wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, tare da raba miliyoyi da muhallansu.

A cikin watan Mayun da ya gabata ne, kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya bai wa Sudan ta kudu wa'adi har zuwa tsakiyar watan Yuli mai kamawa, kan ta kawo karshen yakin basasar da kasar take fama da shi, idan kuma ba haka ta fuksnaci wasu sabbin takunkumai.

Kungiyar IGAD ta bayyana fatan ganin an samu fahimtar juna tsakanin bangarorin gwamnatin Sudan ta kudu da kuma 'yan tawaye a zaman da aka fara gudanarwa a jiya a birnin Khartum, ta mai bayyana hakan a matsayin wata babbar dama da ya kamata dukaknin bangarorin biyu su yi amfani da ita, domin fitar da kasarsu daga mawuyacin halin da ta samu kanta a ciki.

Masu bin diddigin lamurran siyasa a yankin suna ganin cewa, akwai yiwuwar a iya samun ci gaba a wannan tattaunawa, domin kuwa a zaman na jiya an fara duba batutuwa wadanda bangarorin biyu suke da sabani a kansu, ta fuskar ta tafiyar da mulki, da kuma batutuwa na tattalin arziki gami da tsaro, wanda kuma idan suka cimma matsaya a kan yadda za su warware wadannan muhimman batutuwa, to kuwa za a iya cewa an kama hanyar kawo karshen yakin basasar da kasar ta Sudan ta kudu take fama da shi a halin yanzu, kamar yadda ita kanta kasar Sudan take  fatan ganin wannan tattaunawar sulhu da ake gudanarwa a birnin Khartuma  halin yanzu ta haifar da da mai ido, domin hakan na a matsayin wani dutse ne da za ta iya jifar tsuntsaye biyu da shi, na daya dai za ta kara fito da kanta a idon duniya ta fuskar siyasa, tare da tabbatar wa duniya musamman kasashen yammacin turai cewa, a halin yanzu ita mai son zaman lafiya ce, ta yadda har tana daukar nauyin gudanar da zaman sulhuntawa a tsakanin wasu bangarori na ketare da ba su ga maciji da juna, kamar yadda kuma cimma wannan nasara zai ba ta damar ci gaba da fitar wa Sudan ta kudu da danyen manta zuwa gabar ruwa, wanda hakan yake da babban tasiri ga ci gaban tattalin arzikinta.