Sojojin Kasar Somaliya Sun Hallaka 'Yan Ta'addan Kungiyar Al-Shabab Su 7
(last modified Tue, 26 Jun 2018 11:11:42 GMT )
Jun 26, 2018 11:11 UTC
  • Sojojin Kasar Somaliya Sun Hallaka 'Yan Ta'addan Kungiyar Al-Shabab Su 7

Sojojin kasar Somaliya sun ba da labarin cewa a wani gumurzu da suka yi da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Al-Shabab a kudancin kasar, sun sami nasarar hallaka 7 daga cikin 'yan ta'addan.

Kamfanin dillancin labaran Xianhua na kasar China ya ba da labarin cewa sojojin kasar Somaliyan sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da suka fitar inda suka ce sojojin sun yi gumurzu da  'yan kungiyar Al-Shabab din a garin Kismayo da ke kudancin kasar a daya daga cikin maboyarsu mai matukar muhimmanci.

Sojojin sun kara da cewa a yayin gumurzun sun sami nasarar hallaka bakwai daga cikin 'yan ta'addan cikinsu kuwa har da daya daga cikin manyan jagororin kungiyar baya ga wasu biyu kuma da suka kama. Sojojin sun kara da cewa za su ci gaba da wadannan hare-haren har sai sun fatattakin 'yan ta'addan daga wajen.

Tun a shekara ta 2011 ne dai kungiyar Al-Shabab din take rike da wasu bangarori masu yawa na kasar Somaliya duk da cewa daga baya an kwato wasu yankuna masu yawa daga hannunsu.