Afrika : Mutum 2,600 Harin Ta'addanci Ya Kashe A 2017
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32093-afrika_mutum_2_600_harin_ta'addanci_ya_kashe_a_2017
Kimanin hare haren ta'addanci 343 ne aka kiyasta cewa an kai a cikin shekara 2017 da ta gabata a nahiyar Afrika, wadanda suka hadassa mutuwar mutane a kalla 2,600.
(last modified 2018-08-22T11:32:02+00:00 )
Jun 28, 2018 05:21 UTC
  • Afrika : Mutum 2,600 Harin Ta'addanci Ya Kashe A 2017

Kimanin hare haren ta'addanci 343 ne aka kiyasta cewa an kai a cikin shekara 2017 da ta gabata a nahiyar Afrika, wadanda suka hadassa mutuwar mutane a kalla 2,600.

Adadin hare haren dai ya linka sau 22 idan aka kwatanta da wadanda aka kai a nahiyar Turai a shekara data gabata, a cewar ministan harkokin waje na kasar Morocco, Nasser Burita a yankin Shirat.

Mista Burita, na bayyana hakan ne a yayin bude wani taron Darektocin harkokin siyasa na kawancen kasa da kasa dake yaki da kungiyar Da'esh.

Bayannin ya ci gaba da cewa reshe mafi girma na kungiyar Al'Qaida na a nahiyar Afrika, inda yake da mayaka sama da 6,000, inda gungun 'yan ta'adda dake da alaka da wannan kungiya a yammacin Afrika ke da mayaka kimanin 3,500.

Taron dai wata dama ce ta duba hanyoyi da dabaru na bai daya na murkushe kungiyar ta IS, tun daga tushenta a kasashen Iraki da Siriya.