Sudan Ta Kudu : Kiir Da Machar, Sun Amince Da Tsagaita Wuta
(last modified Thu, 28 Jun 2018 05:22:27 GMT )
Jun 28, 2018 05:22 UTC
  •  Sudan Ta Kudu : Kiir Da Machar, Sun Amince Da Tsagaita Wuta

Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir da tsohon mataimakainsa jagoran 'yan tawaye na kasar, Riek Machar, sun amince da shirin tsagaita wuta na tsawan kwanaki uku.

Bangarorin biyu sun cimma wannan matsaya ce a Khartoum, babban birnin kasar Sudan, tare da halartar shugaban kasar Omar el-Béchir.

Wannan dai na zuwa ne bayan haduwar da shugabannin suka yi a birnin Adis Ababa na kasar Habasha a makon da ya gabata, ba tare da cimma wata matsaya ba.

Masharanhanta dai na ganin cewe, wannan babbar alama ce, ta cewa za'a iya cimma yarjejeniyar zaman lafiya, da zata kai ga kawo karshen yakin basasa a wanann jinjira kasa ta Sudan ta Kudu, wanda ya hadassa mutuwar dubban mutane, da kuma cilasta wa milyoyi kaurace wa muhallansu.