Taron Kwamitin Kudi Na Kungiyar AU A Nouakchott
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32096-taron_kwamitin_kudi_na_kungiyar_au_a_nouakchott
Kwamitin ministoci 15 na kungiyar tarayya Afrika, ya fara wani taronsa a Nouakchott, a ci gaba da shirye shiryen taron koli na kungiyar ta AU, karo na 31, da zai gudana daga ranakun 1 zuwa 2 na watan gobe a kasar Mauritania.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jun 28, 2018 00:53 UTC
  • Taron Kwamitin Kudi Na Kungiyar AU A Nouakchott

Kwamitin ministoci 15 na kungiyar tarayya Afrika, ya fara wani taronsa a Nouakchott, a ci gaba da shirye shiryen taron koli na kungiyar ta AU, karo na 31, da zai gudana daga ranakun 1 zuwa 2 na watan gobe a kasar Mauritania.

Ministocin dai za su yi nazari ne kan kudirin kasafin kudin kungiyar ta AU na shekara 2019 mai zuwa, wanda za su mika wa majalisar zartar wa ta kungiyar.

Ministan kudi na Mauritia, Moktar Uld Diay, ya bayyana cewa haduwar zata bada damar duba irin ci gaba da aka samu ta fuskar aiwatar da wasu sauye sauye a fuskar hukumomin kungiyar da kuma irin ci gaba da aka samu ta fuskar manyan ayyukan kungiyar.

Mista Uld Diay ya bayyana wasu daga matsaloli dake zaman karfen kafa ga kungiyar, wandanda suka hada da yawan kudaden da ake bukata da kuma aiwatar dasu.