Masu Zanga-Zanga Sun Afka Wa Gidan Gwamnatin Jahar Plateau
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32105-masu_zanga_zanga_sun_afka_wa_gidan_gwamnatin_jahar_plateau
Wasu matasa sun gudanar da zanga-zangar nuna damuwa kan rikcin da ya faru a jahar Palato, inda suka nufi gidan gwamnati sun kuma farfasa kofofin gilasai da kuma lalata motocin da ke harabar gidan gwamnatin.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jun 28, 2018 17:35 UTC
  • Masu Zanga-Zanga Sun Afka Wa Gidan Gwamnatin Jahar Plateau

Wasu matasa sun gudanar da zanga-zangar nuna damuwa kan rikcin da ya faru a jahar Palato, inda suka nufi gidan gwamnati sun kuma farfasa kofofin gilasai da kuma lalata motocin da ke harabar gidan gwamnatin.

Rahotanni sun ce kungiyar mabiya addinin kirista a Najeriya CAN, ita ce ta bukaci mabiya addinin kirista musamman matasa da kuma iyaye mata da su gudanar da zanga-zanga, domin nuna rashin jin dadin kan abin da ya faru na kashe-kashe a Barikin ladi.

Masu zanga-zangar bayan sun isa gidan gwamnatin jahar Palateau da ke Jos, sun kuma fara farfasa kofofin gilasai da tagogi da lalata motoci, jami'an 'yan sanda sun yi ta lallashin su kan su fice, amma bayan da suka ki amincewa da haka, 'yan sanda sun yi ta harba harsasai cikin samaniyya domin su tarwatsa su.