Rikicin Kabilanci Ya Hallaka Mutum 10 A Habasha
Jun 29, 2018 11:44 UTC
Rahotani dake fitowa daga kasar Ethiopia sun tabbatar da da mutuwar mutum 10 sanadiyar rikicin kabilanci a yammacin kasar
Gidan talabijin da radio na kasar Ethiopia FANA ya sanar da cewa a jiya alhamis wani sabon rikicin kabilanci ya barke a gefen garin Assosa dake yammacin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar lashe rayukan mutum 10 tare da jikkata wasu 56 na daban.
Rahoton ya ce wannan rikici ya dagula al'amura a garin Assousa, kuma ya zuwa yanzu ba a gano musababin rikicin ba.
Cikin wani sabon rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar dangane da kasar ta Habasha a jiya alhamis, ta ce sama da mutune miliyan biyu ne rikicin kabilancin ya raba da gidajensu a kasar ta Ethiopia.
Tags