Najeriya : Gobara Ta Kashe Mutane A Legas
Jun 29, 2018 07:15 UTC
Wata gagarumar wuta da ta faro sanadiyyar hadarin tankar mai a jihar Lagos da ke kudancin Najeriya ta kone tarin motoci da turakun lantarki da ke kan kan hanyar Lagos zuwa Ibadan.
Hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar ta Lagos LASMA ta ce al’amarin ya faru ne a jiya alhamis sanadiyyar wata tankar dakon mai da tun farko ta kama da wuta tare da harbuwa ga tarin motoci fiye da 30 dake kan gadar.
Jami'ai a Najeriya sun ce mutane tara ne suka mutu,daga cikinsu har da karamin yaro,to sai dai wadanda suka shaida lamarin sun ce yawan wanda suka mutun zai iya zarta haka.
Birnin Legas dai shi ne birni mafi girma a nahiyar Afirka, da ke dauke ke da mutane kimanin miliyan 21.
Tags