Najeriya : Buhari Ya Kai Ziyara Katsina Don Jajanta Bala'in Iska
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa jihar Katsina domin jajantawa wadanda bala'in guguwa da ambaliyar ruwa a jihar ya shafa.
Iftila'in dai wanda ya auku a ranakun kurkusa da juna, ya hadassa hasara ra dukiyoyi mai yawa a wasu yankuna na jihar ta Katsina.
A yayin ziyarar shugaba Buhari ya gana da kadan daga cikin wadanda iftila'in ya shafa, a fadar sarkin Katsina.
Ko a ranar Alhamis data gabata, Buhari ya kai irin wannan ziyara a jihar Bauchi domin jajantawa wadanda gobarar da aka yi a kasuwar garin Azare ta shafa da kuma bala'in guguwa a jihar, wanda ya hadassa mutuwar mutane da dama da da jikkatar wasu masu yawa da kuma lalata dukiyoyi.
Saidai a yayin da wasu ke danganta wadanan ziyarce ziyarce na Shugaba Buhari na alama ta murmurewa daga rashin lafiyar da ya yi fama da shi, wasu da danganta hakan sukayi da siyasa idan akayi la'akari da zabukan kasar dake tafe.