Kwana Na Biyu A Taron Kungiyar AU
Jul 02, 2018 06:41 UTC
Yau kwana na biyu kuma na karshe kenan da shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashen Afrika ke halartar taron kunsgiyar tarayyar Afrika karo na 31 a birnin Nouakchott na kasar Mauritania.
Taron dai na maida hankali ne kan batutuwa da dama da suka hada da tsaro, da batun tsarin nan na cinikayya marar shinge a tsakanin kasashen nahiyar.
A wani lokaci nan gaba ne ake sa ran shugaban kasar Faransa Emanuel Macron, zai gana da shugabanin kasashen gungun G5 Sahel da aka kafa don yaki da ta'addanci, kan matsalar tsaro wadda ke ci gaba da tabarbarewa, yayin da a baya-bayan nan aka kai sabon farmaki kan sojojin Faransa a Mali, da kuma a shalkwatar tsaron rundinar ta G5 Sahel a tsakiyar Mali.
Tags