Nijeriya : Kotu Ta Sake Ba Da Umarnin A Saki Sambo Dasuki
Wata babbar kotun Abuja a tarayya Najeriya, ta bayar da umarnin a saki tsohon mai bai wa shugaban Kasar shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, wanda ake tsare da shi bisa zargin handame kudaden da aka warewa domin sayen makaman yaki da 'yan Boko Haram.
Mai shari'a Ijeoma Ojukwu, ta ce a saki Dasuki, idan ya bayar da naira miliyan 200 da kuma mutum biyu da za su tsaya masa, wadanda dole su kasance ma'aikatan gwamnatin tarayya wadanda matakin aikinsu bai gaza mataki na 16 ba.
Duk da cewa babu tabas akan ko gwamnatin za ta amince da bada belinsa, amma lauyen Dasukin, Ahmed Raji ya ce, tun daga yau Talata, za su fara nazari kan sharuddan da kotun ta gindaya musu don fara korarin ganin sun cika su.
Dasuki, wanda a baya kotun tarayyar ta bayar da belinsa sau hudu, ban da belinsa da kotun ECOWAS ta bayar, ya nemi kotun ta tilasta wa gwamnatin tarayya ta bi dukkan umarnin kotun da aka bayar na sakinsa, saidai gwamnatin ta nace cewa tana rike da shi ne saboda ta daukaka kara.