An Fara Tattauna Batun Karawa Shugaban Kasar Sudan Ta Kudu Wa'adin Mulki
Yan Majalisun Dokokin Kasar SUdan ta Kudu sun fara gudanar da muhawara kan karawa shugaban kasar Sudan ta Kudu Silva Kiir wa'adin mulki zuwa shekara ta 2021.
A jawabin da ya gabatar a gaban Majalisar Dokokin Kasar Sudan ta Kudu a jiya Litinin: Ministan Shari'ar kasar Paulino Wanawilla Unango ya bukaci karin wa'adin mulkin shugaban kasar Silva Kiir da na mataimakinsa gami da na 'yan Majalisun Dokokin Kasar zuwa watan Yulin Shekara ta 2021.
A halin yanzu haka an mika daftarin kudurin zuwa gaban kwamitin Majalisar Dokokin Kasar domin yin nazari kafin maido shi zuwa gaban Majalisar Dokokin Kasar domin gudanar da muhawara.
Bukatar karin wa'adin har na tsawon shekaru uku nan gaba ya zo ne sakamakon irin halin rashin tabbas da kasar take ciki tun bayan bullar yakin basasa a watan Disamban shekara ta 2013 bayan da kasar ta samu 'yancin gashin kai daga kasar Sudan a shekara ta 2011.