Najeriya: An Kashe 'Yan Sanda 7 A Abuja
Wasu ‘yan fashi da makami sun kashe jami’an ‘yan sandan Najeriya bakwai a Abuja babban birnin kasar.
Rahotanni dake fitowa daga Nigeriya sun habarta cewaa yammacin yau Talata wasu 'yan fashi da makami sun kai hari kan jami'an 'yan sanda a mahadar hanyar Galadimawa da ta ratsa hanyar filin jiragen sama na kasa da kasa, inda suka she bakwai daga cikinsu.
Kwamishinan ‘yan sandan birnin Abuja, Sadiq Bello ya tabbatar wa manema labarai da aukuwar lamarin duk da cewa bai bada cikakken bayani ba.
Tuni aka kwashe gawarwakin 'yan sandan, yayin da mazauna yankin suka shiga halin fargaba.
Bayanai na cewa, 'yan fashin da ke cikin mota sun far wa 'yan sandan ne cikin ba-zata a dai dai lokacin da suke bakin aiki.
Wannan lamari na zuwa ne kwanaki uku kacal da aka kashe wasu jami’an ‘yan sanda a Akwa Ibom da ke kudancin kasar.