An Bukaci Karin Wa'adin Shugaban Kasa Da Majalisa A Sudan Ta Kudu
'Yan Majalisar kasar Sudan ta kudu sun fara tattaunawa kan yadda za a yiwa kundin tsarin milkin kasar kwaskwarima ta yadda za a kara wa'adin shugaban kasa da na 'yan Majalisa zuwa shekara ta 2021.
A jawabin da ya gabatar a gaban Majalisar Dokokin Kasar Sudan ta Kudu a jiya Litinin: Ministan Shari'ar kasar Paulino Wanawilla Unango ya bukaci karin wa'adin mulkin shugaban kasar Silva Kiir da na mataimakinsa gami da na 'yan Majalisun Dokokin Kasar da kuma na Gwamnoni zuwa watan Yulin Shekara ta 2021.
Paul Youni Bunjo shugaban kwamitin sadarwa na Majalisar kasar ya yi ishara da cewa shugaban Majalisar ya gabatar da wannan daftari zuwa ga kwamitin dokoki na Majalisar, inda ya ce bayan kamala zaman kwamitin zai gabatar da sakamakon zaman zuwa ga shugaban majalisar kasar Sudan ta Kudun.
Bukatar karin wa'adin har na tsawon shekaru uku nan gaba ya zo ne sakamakon irin halin rashin tabbas da kasar take ciki tun bayan bullar yakin basasa a watan Disamban shekara ta 2013 bayan da kasar ta samu 'yancin gashin kai daga kasar Sudan a shekara ta 2011.