Tashin Bam A Babban Birnin Somaliya
(last modified Tue, 03 Jul 2018 18:10:58 GMT )
Jul 03, 2018 18:10 UTC
  • Tashin Bam A Babban Birnin Somaliya

Majiyar kasar Somaliya ta sanar da tashin Bom a Magadushu babban birnin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar mutane bakwai.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto 'yan sandar Somaliya na cewa a jiya Litinin wani Bam ya tashi a anguwar Binadir na birnin Magadushu, lamarin da ya yi sanadiyar jikatar mutane bakwai.

A ranar Lahadin da ta gabata ma, kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab ta kai harin roka a kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 4.

Kungiyar Ashabab mai alaka da kungiyar ta'addancin nan ta Alqa'ida wacce a shekaru baya take rike da yankuna da dama na kasar Somaliya ta rasa yankuna da dama a shekarar 2011 bayan da  Dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen  Afirka suka shiga kasar, suka kuma fatattake su daga wasu manyan buranan kasar.

Kungiyar ta'addanci ta al-shabab tana a matsayin babbar barazana ga tsaron Somalia da kuma sauran kasashen makwabta.