Shugaban kasar Faransa Ya Fara Ziyara A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32190-shugaban_kasar_faransa_ya_fara_ziyara_a_najeriya
A jiya talata ce, Shugaban kasar Faransa Emanuel Macron ya fara ziyara a Nijeriya, inda a yayin ganawarsa da Shugaba Buhari ya yi alkawarin taimakawa Najeriya a yakin da ta'addanci.
(last modified 2018-08-22T07:02:03+00:00 )
Jul 04, 2018 07:28 UTC
  • Shugaban kasar  Faransa Ya Fara Ziyara A Najeriya

A jiya talata ce, Shugaban kasar Faransa Emanuel Macron ya fara ziyara a Nijeriya, inda a yayin ganawarsa da Shugaba Buhari ya yi alkawarin taimakawa Najeriya a yakin da ta'addanci.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi alkawarin bayar da tallafin Dalar Amurka miliyan 75 don ci gaba da yaki da kungiyar Boko Haram a Najeriya da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita.

Macron wanda a karon farko kenan da yake ziyartar Najeriya a matsayin shugaban kasa, ya ce, gwamnatinsa za ta kuma bai wa Najeriyan bashin kudaden da yawansu ya kai Dala miliyan 475 don inganta harkokin sufuri a jihar Legas da samar da ruwan sha mai tsafta a jihar Kano, yayin da kuma za a bunkasa gandun dajin da ke jihar Ogun.

Gabanin ziyararsa a Najeriya, shugaba Macron ya gana da shugabannin kasashen Afrika a taron da suka gudanar a Mauritania, taron da ya mayar da hankali kan sha’anin tsaro a kasashen yankin Sahel da ke fama da rikicin Boko Haram.