Sudan Ta Musunta Bayanin Amurka Na Cewa Akwai Barazanar Tsaro A kasar
(last modified Wed, 04 Jul 2018 21:20:46 GMT )
Jul 04, 2018 21:20 UTC
  • Sudan Ta Musunta Bayanin Amurka Na Cewa Akwai Barazanar Tsaro A kasar

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta nuna rashin jin dadi dangane da wani bayani da ofishin jakadancin Amurk a Khartum ya bayar, da ke kiran Amurkawa da su yi taka tsantsan danagen ad zuwa wasu yankunan kasar ta Sudan, saboda dalilai na tsaro.

Bayanin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sudan ya ce babu gaskiya a cikin abin da ofishin kadancin Amurka ya fada, kan cewa akwai barazanar ayyukan ta'addanci a yankunan darfur, Kurdufan da kuma Nail azraq.

Haka nan kuma ma'aikatar harkokin wajen ta Sudan ta ce, Amurkawa suna shiga cikin dukkanin wadannan yankuna ba tare da sun taba fuskantar wata barazana ba.

Ofishin jakadancin na Amurka ya gargadi wata tawagar Amurka da ta isa Sudan kan ta yi hattara, domin akwai yiwuwar su fuskanci hare-hare a  wadannan yankuna, lamrin da ya bakanta wa gwamnatin Sudan.