Rikicin APC: Bolaji Da Oshomole Sun Yi Magana Kan Sabuwar APC
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32201-rikicin_apc_bolaji_da_oshomole_sun_yi_magana_kan_sabuwar_apc
Shugaban jam'iyyar APC mai mulki a tarayyar Nigeria Adams Oshomole ya bukaci yayan jam'iyyar wadanda suka yi fushi da ita su yi hakuri don a shrye yake ya sauraresu.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jul 05, 2018 07:17 UTC
  • Rikicin APC: Bolaji Da Oshomole Sun Yi Magana Kan Sabuwar APC

Shugaban jam'iyyar APC mai mulki a tarayyar Nigeria Adams Oshomole ya bukaci yayan jam'iyyar wadanda suka yi fushi da ita su yi hakuri don a shrye yake ya sauraresu.

Jaridar Primiumtimes ta Najeriya ta Nakalto Oshomole yana fadar haka bayan da wasu yan jam'iyyar suka bayyana bellewar su a jiya Larabawa daga babbar Jam'iyyar. 

Har'ila yau kakakin jam'iyyar Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa a shirye suke su saurari korafe -korafen yayan sabuwar jam'iyyar mai suna R-APC wato jam'iyyar APC wacce aka yiwa koskorima . 

A jiya larabane Buba galadima shugaban sabuwar Jam'iyyar ta R-APC ta kasa ya bada sanarwan cewa kafa sabuwar jam'iyyar ta R-APC. 

Korafe korafen sabuwar jam'iyyar dai sun hada da Zaben Oshiomole a matsayin shugaban jam'iyyar da kuma wasu mukamai 17 ba tare da bin tsarin da ya dace a cikin jam'iyyar ba.