Najeriya: Jam'iyyar APC Na Tuntubar R-APC Domin A Sasanta
Jam'iyyar APC mai mulki a Najerya ta bayyana cewa tana ci gaba da tuntubar bangaren da ya shelanta ballewa tare da kafa wani bangare a jam'iyyar mai suna R-APC karkashin jagorancin Alh. Buba Galadima, domin sasantawa.
A ta bakin jami'in hulda da jama na jam'iyyar APC mai mulki Kabiru Masari, suna ci gaba da tuntubar bangaren da ya yi fushi a cikin jam'iyyar, kuma suna fatan za a sasanta.
Wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar ta APC ne dai suka kafa wani bangare mai suna sabuwar APC waro R-APC, domin fuskantar abin da suka kira nuna banbanci da ake yi a cikin jam'iyyar.
Tun kafin wannan lokacin dai wasu daga cikin manyan 'ya'yan jam'iyyar sun yi barazanar ballewa matukar ba a gyara abin da suka kira kurakuran da ake tafkawa a cikin jam'iyyar ba.