Kotun Kolin Tarayyar Najeriya Ta Wanke Bukola Saraki
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32214-kotun_kolin_tarayyar_najeriya_ta_wanke_bukola_saraki
A yau ne kolin tarayyar Najeriya ta wanke shugaban majalisar dattijai Alh. Abubakar Bukola Saraki daga sauran tuhumcetuhumce uku daga cikin 18 da suka rage a kansa, kan rashin bayyana gaskiya kan kaddarorin da ya mallaka.
(last modified 2018-08-22T07:02:04+00:00 )
Jul 06, 2018 12:56 UTC
  • Kotun Kolin Tarayyar Najeriya Ta Wanke Bukola Saraki

A yau ne kolin tarayyar Najeriya ta wanke shugaban majalisar dattijai Alh. Abubakar Bukola Saraki daga sauran tuhumcetuhumce uku daga cikin 18 da suka rage a kansa, kan rashin bayyana gaskiya kan kaddarorin da ya mallaka.

Shafi jaridar sahara Reporters ya habarta cewa, a zaman kotun da aka gudanar yau, kotun ta yi watsi da dukkanin tuhumce-tuhumcen da gwamnati ta gabatar a kansa, tare da bayyana shi a matsayin maras laifi.

Abubakar Bukola Saraki ya yi murna da wannan babbar nasara da ya samu, inda ya kayar da gwamnatin Najeriya  a gaban kotu, inda ya bayyana cewa, dukkanin abin da ya faru dama magana ce ta siyasa, kuma an yi masa haka ne domin cin zarafinsa saboda samun mukamin shugaban majalisar dattijai da ya yi, wanda wasu ba su yi murna da hakan ba.

Kamar yadda kuma ya gode ma dukkanin 'yan majalisar dattijai da na wakilai da suka mara masa tun daga farkon shari'ar har zuwa karshenta.