Ruwanda : An Yanke Hukunci Mai Tsauri Kan Wasu Mayan Sojoji
-
Shugaba Paul Kagame na Ruwanda
Wata kotun Soji a Ruwanda ta yanke hukuncin zamen gidan yari na shekaru 20 zuwa 21 ga wasu mayan sojin kasar biyu saboda neman tada zamne tsaye a kasar.
kotun ta yanke ma kanal Tom Byabagamba hukuncin zamen gidan yari na shekrau 21, yayin da ta yanke na shekaru 20 ga janar Frank Rusagara mai ritaya inji alkalin kotun Narcisse Nsengiyumva.
Janar Rusagaraya ya taba rike mukamin sakatare janar na ministan tsaro kasar, shi kuwa kanal Byabagamba ya taba jagorantar rundinar tsaron fadar shugaban kasa.
An dai tsare su a watan Agusta shekara 2014 saboda neman tada zamne da bata sunan kasa da kuma yiwa gwamnatin zagon kasa.
Alkalin daya jagoranci shari'a ya ce yana da kwararen hujojin dake tuhumar mutanen.