MDD: Har yanzu Ana Cin Zarafin 'Yan Adam A Sudan Ta Kudu
Kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya sanar da cewa, har yanzu ana aiwatar da ayyukan cin zarafin 'yan adama a wasu sassa na kasar Sudan ta kudu.
A rahoton da kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya fitar a yammacin jiya, an sanar da cewa, yanzu haka akwai yara da mata da ake aikata laifukan yaki a kansu a wasu yankuna da suke karkashin gwamnati, kamar yadda kuma hakan take faruwa a wasu yankuna da ke hannun 'yan tawaye.
Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya yi gargadin cewa idan gwamnatin Sudan ta kudu da kuma 'yan adawa ba sulhunta kansu ba, to za a kakaba musu takunkimi.
A makon da ya gabata ne aka cimma matsaya kan raba madafun iko tsakanin bangarorin biyu, amma har yanzu ba a cimma daidaito kan batun mukaman ba.