Sudan Ta Kira Jakadan Kungiyar Tarayyar Turai
Bayan watsa wani bayyani na kungiyar tarayyar Turai game da wajibci kame shugaban kasar Sudan, Ma'aikatar harakokin wajen kasar ta kira jakadan Kungiyar tarayyar Turai dake birnin Khartoum.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa ma'aikatar harakokin wajen kasar Sudan ya kira Jean Michel Dumond jakadan kungiyar tarayyar Turai a birnin Khartoum, domin nuna masa rashin jin dadinta kan bayyanin da kungiyar tarayyar turan ta fitar a game da shugaban kasar Omar Al-Bashir.
Karibulla.. Alkhadar kakakin ma'aikatar harakokin wajen kasar Sudan ya ce a tattaunawar da aka yi tsakanin jakadan kungiyar ta Turai da mataimakin ministan harakokin wajen kasar Abdulgani Alhakim, jakadan na turai ya karyata cewa kungiyar kasashen Turai na matsin lamba ga kasashen Afirka a kan su kama shugaban Sudan Omar Al-Bashir.
Cikin wata sabuwar sanarwa da ta fitar, kungiyar tarayyar Turan ta bayyana takaicinsa ga kasashen Djibouti da Uganda na rashin kama shugaba Al-Bashir a yayin da ya kai ziyara kasashensu, su kuma meka shi ga kotun hukunta manya laifuka ta kasa da kasa.