Sudan Ta Kudu : An Tsawaita Wa'adin Mulkin Salva Kiir
Majalisar dokokin Sudan ta Kudu, ta amince da dokar tsawaita wa'adin mulkin hukumomin rikon kwarya na kasar da shekaru ukku, ciki har da na shugaban kasar Salva Kiir.
Tuni dai aka fara ganin wannan matakin zai iya kawo cikas ga tattaunawar zaman lafiyar da ake a wannan jinjirar kasar.
Tun a shekarar 2015 ne Sudan ta Kudu,ke karkashin gwamantin wucin gadi, kamar yadda yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma ta tanada a waccen lokacin.
A yarjejeniyar ta waccen lokacin a watan Agusta na wannan shekara ta 2018 ne wa'adin mulkin hukumomin kasar harda na bangaren majalisa ke kawo karshe.
A wanann shekarar ce kuma aka tsara gudanar da manyan zabukan kasar, saidai rikicin da kasar ke fama dashi tun shekara 2013, ya kawo cikas wajen gudanar da zabukan, wanda hukumomin suka ce ba za'a iya kyale kasar ba babu shugabanci, dole a tsawaita wa'adin hukumomin kasar.