An Damu game da zarge zargen fyade a Afrika ta Tsakiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3232-an_damu_game_da_zarge_zargen_fyade_a_afrika_ta_tsakiya
Babban kwamishinan MDD kan harkokin 'yancin dan adam, Zeid Ra'ad Al Hussein, ya ce abun damuwa ne zarge zarge baya bayan nan na fyade da cin zarafin mata da sojojin MDD, Faransa da masu dauke da makamai dake Afrika ta Tsakiya suka aikata.
(last modified 2018-08-22T06:58:04+00:00 )
Apr 01, 2016 02:07 UTC
  • Mr Zaid Ra\'ad Al\'Hussein babban kwamishinan hukumar kare hakin dan adam ta MDD
    Mr Zaid Ra\'ad Al\'Hussein babban kwamishinan hukumar kare hakin dan adam ta MDD

Babban kwamishinan MDD kan harkokin 'yancin dan adam, Zeid Ra'ad Al Hussein, ya ce abun damuwa ne zarge zarge baya bayan nan na fyade da cin zarafin mata da sojojin MDD, Faransa da masu dauke da makamai dake Afrika ta Tsakiya suka aikata.

An samu muhimmin cigaba domin gudanar da bincike kan wadannan zarge zarge da tawagogin ma'aikatan MDD da dama da aka tura a wannan yanki suka gano a 'yan makwanni biyu da suka gabata, in ji mista Zeid, a cewar wata sanawa ta ranar Alhamis.

"MDD za ta yi iyakacin kokari domin gudanar da bincike kan wadannan zarge zarge na wuce gona da iri, da suka shafi wasu ayyukan fyade kan mata da 'yan mata masu yawa a wannan kasa.