An Tsawaita Wa'adin Tawagar Sulhu Ta MDD A Sudan
Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya kara wa'adin aikin dakarun majalisar dinkin duniya na kungiyar tarayyar Afrika a kasar Sudan.
A zaman da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar a jiya, dukkanin mambobin kwamitin 15 sun kada kuri'ar amincewa da kara wa'adin aikin dakarun wanzan da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya da na AU a kasar Sudan.
Kudirin kara wa'adin aikin dakarun na majalisar dinkin duniya da kuma tarayyar Afrika a Sudan mai lamba 2429, ya bayar da dama ga wadannan dakaru kan su ci gaba da aikinsu a Sudan har zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2019.
Dakarun na MDD da na tarayyar Afrika suna gudanar da ayyukan hadin gwiwa ne domin tabbatar da sulhu da zaman lafiya a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan.