An Tsawaita Wa'adin Tawagar Sulhu Ta MDD A Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32321-an_tsawaita_wa'adin_tawagar_sulhu_ta_mdd_a_sudan
Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya kara wa'adin aikin dakarun majalisar dinkin duniya na kungiyar tarayyar Afrika a kasar Sudan.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jul 14, 2018 08:00 UTC
  • An Tsawaita Wa'adin Tawagar Sulhu Ta MDD A Sudan

Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya kara wa'adin aikin dakarun majalisar dinkin duniya na kungiyar tarayyar Afrika a kasar Sudan.

A zaman da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar a jiya, dukkanin mambobin kwamitin 15 sun kada kuri'ar amincewa da kara wa'adin aikin dakarun wanzan da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya da na AU a kasar Sudan.

Kudirin kara wa'adin aikin dakarun na majalisar dinkin duniya da kuma tarayyar Afrika a Sudan mai lamba 2429, ya bayar da dama ga wadannan dakaru kan su ci gaba da aikinsu a Sudan har zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2019.

Dakarun na MDD da na tarayyar Afrika suna gudanar da ayyukan hadin gwiwa ne domin tabbatar da sulhu da zaman lafiya  a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan.