An Ceto Mutane Da Dama Daga Hanun Masu Fataucin Mutane A Sudan
Hukumomin Kasar Sudan sun sanar da kwato Mutane kimanin 140 daga hanun masu fataucin mutane zuwa kasashen Turai.
Kamfanin dillancin Labaran Irna ya nakalto wani jami'in kasar Sudan na cewa jami'an tsaron kasar sun samu nasarar kwato mutane 139 daga hanun msu fataucin mutane zuwa kasashen Turai a jahar Kasala dake gabashin kasar.
Jami'in ya ce 'yan sanda sun cabke wani gungu daga cikin fataucin mutanan zuwa Turai.
A nasa bangare Adam Jama'a gwamnan jahar Kasala ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa masu yaki da fataucin Mutane su taimakawa kasarsa wajen magance wannan matsala, domin a cewarsa Mata da kananen yara na cikin hatsari na masu safarar mutanan zuwa kasashen Turai da na Larabawa.
A farkon shekarar 2017 ne Majalisar dokokin kasar Sudan ta samar da dokar kisa ko daurin shekaru daga 5 zuwa 20 ga masu fataucin mutane ko kuma cinikayyarsu a kasashen waje.