Shugaban Tunusiya Ya Jadadda Shirin Kasarsa Na Farfado Da Harkar Tattalin Arzikinta
Shugaban kasar Tunusiya ya jaddada aniyar kasarsa ta ci gaba da farfado da harkar siyasa da bunkasa tattalin arzikinta.
A jawabin da fadar shugaban kasar Tunusiya ta fitar ta bayyana cewa: A ganawar da ta gudana tsakanin shugaban kasar ta Tunusiya Beji Qa'id Essebsi da ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Yves Le Drian a fadar Carthage ta kasar Tunusiya a jiya Lahadi, bangarorin biyu sun tattauna batun gudanar da ayyuka tare a fannoni da dama gami da halin da ake ciki a kasar Libiya musamman hanyoyin da suka dace a bi wajen warware rikicin siyasar kasar ta Libiya ta hanyar lumana.
Har ila yau Jean-Yves Le Drian ya jaddada bukatar gudanar da taimakekkeniya a tsakanin kasashen Faransa da Tunusiya tare da jaddada bukatar goya baya wa kasar ta Tunusiya a fagen siyasa da tattalin arziki.