An Hallaka 'Yan Ta'addar Al-Shabab 87 A Kudancin Somaliya
(last modified Tue, 24 Jul 2018 19:15:25 GMT )
Jul 24, 2018 19:15 UTC
  • An Hallaka 'Yan Ta'addar Al-Shabab 87 A Kudancin Somaliya

Gwamnatin Somaliya ta sanar da hallaka mayakan Al-Shabab 87 yayin arangama da jami'an tsaro a kudancin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya nakalto Adnan Ishaq Ali, mataimakin ministan sadarwa na kasar Somaliya na cewa jami'an tsaron kasar sun samu nasarar hallaka mayakan Al-Shabab 87 a yayin wata arangama da suka yi a kudancin kasar, inda a bangaren jami'an tsaron,  sojoji  biyar na sansanin sojan Bar-Sanguni suka rasa rayukansu.

Majiyar gwamnatin dai ta ce 'yan ta'addar sun fara kai harin ne ,da tayar da wasu motoci biyu shake da bama-bamai a sansani sojan na Bar-Sanguni dake kudancin kasar.

Kungiyar ta'addanci ta al-shabab tana a matsayin babbar barazana ga tsaron Somalia da kuma sauran kasashen makwabta.

Tun bayan shigar kungiyar wanzar da zaman lafiya na kasashen Afirka a shekarar 2011, suka fatattaki mayakan kungiyar ta Al-shabab daga wasu manyan burane da ma kauyukan kasar da suka mamaye a baya.