Nigeria Da Niger Sun Kulla Yerjejeniyar Gina Matatar Katsina
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32468-nigeria_da_niger_sun_kulla_yerjejeniyar_gina_matatar_katsina
A jiya Talata ce gwamnatin tarayyar Nigeria da ta jumhuriyar Niger suka rattaba hannun kan yerjejeniyar gina matatar man fetur da bututun sinadarin hydrocarbon a Katsina.
(last modified 2018-08-22T07:02:09+00:00 )
Jul 25, 2018 01:54 UTC
  • Nigeria Da Niger Sun Kulla Yerjejeniyar Gina Matatar Katsina

A jiya Talata ce gwamnatin tarayyar Nigeria da ta jumhuriyar Niger suka rattaba hannun kan yerjejeniyar gina matatar man fetur da bututun sinadarin hydrocarbon a Katsina.

Jaridar Dailytrust ta Nigeria ta bayyana cewa shugaban tarayyar Nigeria Muhammadu Buhari da tokoransa na Jumhuriyar Niger Mohmmad Yusu ne suka shaida bikin rattaba hannun kan wannan yerjejeniyar, wanda ministan man fetur na Nigeria Dr Ibe Kachikwu da kuma ministan makamshi da man fetur na jumhuriyar Niger Foumakoye Gado suka sanyawa hannu a madadin kasashensu a fadar shugaban kasa a Abuja.

Ana saran matatan man na Katsina zai samar da tataccen man fetur gan dubu 100-150 a ko wace rana idan an kammala aikin ginata. Banda haka an kafa komitin kula da yadda aikin gina matatan zai tafi tare da shugabannin ministocin man fetur na kasashen biyu na karba karba. A bangaren guda kuma an kafa komitin tsara yadda aikin zai tafi karkashin shugabancin Injiniya  Rabiu Suleiman na Nigeria da kuma mataimakinsa babban daractan kamfanin Hydrocarbon na Niger.

Kamfanin haka da sarrafa man fetur mallakin kasar China CNPC a takaice yake haka da sarrafa man fetur a matatar man fetur ta Soraz. Kuma kamfanin ya ce ya kara yawan man fetur da yakem haka a shekara ta 2018 daga ganga dubu 50,000 a ko wace rana zuwa ganga dubu 70,000.  

Ba'a bayyana yawan kudaden da aikin zai lakume ba sai bayan karban rahoton komitin aiwatar da aikin ya shigo hannu.